Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-31 19:18:23    
Kasar Sin za ta shirya aikace-aikacen tunawa da cika shekaru 60 da jama'ar kasar Sin suka samun nasara a cikin yakin yin adawa da mhara na Japan

cri

Shekarar nan shekara ce ta cikon shekaru 60 da jama'ar kasar Sin suka samun nasara a cikin yakin yi adawa da mahara na Japan, kuma kasashen duniya suka samun nasara a cikin yakin yi adawa da Fascist. Ran 30 ga wata, wakilinmu ya samo labari daga taron watsa labaru da offishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin cewa, kasar Sin za ta shirya aikace-aikacen tunawa da wannan rana a jere daga ran 2 zuwa ran 3 ga wannan wata domin tunawa da nasarar da jama'ar kasar Sin da mutane masu ra'ayin cigaba na kasashen duniya suka samu ta hanyar yin yake-yake sosai. Yanzu, ga cikakken labarin da wakilinmu ya ruwaito mana:

Ran 2 ga watan Satumba na shekarar 1945, gwamnatin Japan ta sa hannu a kan takardar ba da kai, hakan ya sa an kawo karshen yakin yin adawa da Fascist na duniya . Kuma ran 3 ga watan Satumba ta zama ranar tunawa da nasarar da kasar Sin ta samu a cikin yakin yin adawa da Japan. Mr. Chen Haosu, shugaban majalisar sada zumunta da kasashen waje na kasar Sin ya bayyana cewa, nasarar da jama'ar kasar Sin suka samu a cikin yakin yin adawa da Fascist na duniya sakamakon rasa mutane da dukiyoyi masu yawa, tana da ma'ana sosai, kuma ta isa a tuna da ita:

"Yakin yin adawa da mahara na Japan da jama'ar kasar Sin suka yi shi ne wani muhimmin sashe na yakin yin adawa da Fascist na duniya, muna iya cewa, ya ba da taimako sosai a kan zaman lafiya da samun ci gaba na jama'a, wannan wani babban abin tunawa ne. Dalilin da ya sa muka shirya aikace-aikacen tunawa da wannan ranar shi ne domin nuna wannan babban abin tunawa ga dukan duniya."

Bisa labarin da muka samu an ce, aikace-aikacen tunawa da ranar da za a shirya suna da yawa, a cikin shagalin dare na nuna wasannin fasaha a ran 2 ga watan Satumba, da kuma babban taron tunawa da za a shirya a ran 3 ga watan Satumba, akwai mutane fiye da 6000 da za su halarci ko wanesu. Yawan mutanen da za su halarci aikin ba da kwandon furanni da za a yi a ran 3 ga watan Satumba, zai kai fiye da dubu 10. Bayan haka kuma wannan aiki zai mai da hankali kan tsofaffin sojoji na kasar Sin da na waje da suka halarci wannan yaki, ran 2 ga watan Satumba, akwai tsofaffin soja na kasar Sin da na waje da suka halarci yakin yin adawa da Japan da yawansu ya kai fiye da 400 za su halarci aikin sa hannu da bikin bude bangon zaman lafiya na duniya a nan birnin Beijing, kuma masu halartar bukin za su daddale sanarwar zaman lafiya ta Beijing, Mr. Chen Haosu ya ce, wadannan aikace-aikacen jama'a za su bayyana fatan tsoffafin sojoji kan kaunar zaman lafiya, da darajanta zaman lafiya:

"Kaunar abokantaka mai zurfi daga mutane tana da daraja sosai. Wadannan tsoffafin sojojin da suka halarci yakin yin adawa da Fascist, musamman tsofaffin sojojin da suka zo kasar Sin don halartar yakin yin adawa da Japan, sun samu nasarar zaman lafiya ta yin kokari tare da jama'ar kasar Sin. Nan gaba, za su yi hadin kai, kuma tare da jama'ar kasashen duniya, don samun nasara ta hanyar hana yaki."
Mr. Wang Guoqing, mataimakin shugaban offishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi bayani a gun taron watsa labaru cewa, ya kamata a ci gaba da matakin yi hadin gwiwa da kasar Sin da kasashe dabam daban suka dauka a lokacin yaki har zuwa lokacin zaman lafiya.

"Wannan halin nacewa na kasar Sin da kuma matakin yin hadin gwiwa da kasashen duniya, ba kawai suna da amfani a shekaru 60 da suka wuce ba, kuma nan gaba za mu ci gaba da yin amfani da su. Sabo da haka, wannan kuma darasi ne mai daraja sosai da ya kamata mu iya samu a cikin yaki."

Mr. Wang Guoqing ya ce, jama'ar kasar Sin ba za ta manta da wadancan mutanen da suka ba da taimakonsu da kuma rasa rayukansu domin kafa sabuwar kasar Sin ba. (Bilkisu)