A ran 29 ga watan nan a nan birnin Beijing, an bude taro domin tunawa da cikon shekaru 10 da aka kira babban taron matan duniya na hudu na Majalisar Dinkin Duniya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana a gun bikin bude taron, cewa tun bayan da aka yi babban taron matan duniya na hudu, an samu babban ci gaba a fannin matan kasashen daban daban, kuma kasar Sin za ta yi kokari tare da mutanen kasashen daban daban domin sa kaimi ga samun daidaici tsakanin maza da mata da tabbatar da hakki da moriyar mata da kuma bayar da sabuwar gudummowa ga bunkasuwar sha'anin matan duniya. Yanzu ga labarin da wakilinmu ya rubuto mana filla filla.
An bude babban taron matan duniya na hudu na Majalisar Dinkin Duniya a cikin shekara ta 1995 a nan birnin Beijing. Mutane fiye da dubu 40 sun halarci taron wanda aka fi samun yawan wakilan kungiyoyin gwamnati da na kugiyoyin da ba na gwamnati ba a gun taron Majalisar Dinkin Duniya. Kuma an zartas da Sanarwar Beijing da Ka'idojin aiwatarwa a gun taron domin tabbatar da cewa samun daidai wa daida tsakanin maza da mata da kuma bayar da mata hakkinsu su ne muhimman abubuwa kan samun bunkasuwa da zaman lafiya. A cikin shekaru 10 da suka gabata, an yi ta shaida muhimman ma'ana da amfani na wancan taro kan raya sha'anin matan duniya.
A ran 29 ga wata, an bude taro domin tunawa da cikon shekaru 10 da aka kira babban taron matan duniya na hudu na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi mai muhimmanci a gun bikin bude taron. Yayin da ya jaddada muhimmiyar ma'anar kiran taron, ya ce,
1 2 3
|