Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-29 15:34:54    
Ba a iya tabbatar da makomar sabon tsarin mulkin kasar Iraq ba

cri

Ran 28 ga watan nan majalisar jama'ar wucin gadi ta kasar Iraq ta amince da sabon shirin tsarin mulkin kasar da kwamitin tsara tsarin mulkin kasar ya bayar a ran nan, amma darikar Sunni ta ki amincewa da wannan shiri.

Majalisar jama'ar rikon kwarya ta kasar ba ta kada kuri'a kan shirin tsarin mulkin kasar a ran nan ba. A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a ran nan, shugaban kasar Iraq Jalal Talabani ya bayyana cewa, an riga an bayar da shirin tsarin mulkin kasar, ba a bukatar a kada kuri'a kan wannan, za a jefa kuri'ar raba gardama kan wannan shiri a daidai lokacin da aka tsara a da, wato a tsakiyar kwanaki 10 na watan Oktoba na shekarar da muke ciki, a kasar Iraq. Ya kuma yi kira ga jama'ar kasarsa da su amince da wannan shiri, ta yadda kasar Iraq za ta taka sabon mataki lami lafiya ne a fannin ayyukan siyasa.

Shugaban kasar Amurka Bush ya yaba wa kasar Iraq sosai saboda ta gabatar da sabon shirin tsarin mulkin kasar, wannan mataki ne da kasar Iraq ta taka wajen shimfida dimokuradiyya a duk kasar da kuma wata nasara ce da masu bin dimokuradiyya ta ci wajen yaki da masu tsagerun ra'ayi. Ya kuma yi kira ga 'yan kasar Iraq da su sa hannu cikin ayyukan siyasa cikin himma da kwazo, haka kuma su yanke shawara yadda ya kamata a cikin kada kuri'ar raba gardama da za a yi a tsakiyar kwanaki 10 na watan Oktoba na shekarar da muke ciki.

Ko da yake kafin ya ba da shirin tsarin mulkin kasar ga majalisar jama'ar kasar a ran 28 ga watan nan, kwamitin tsara tsarin mulkin kasar ya sake yin kwaskwarima ga wannan shiri, amma wakilai 15 na darikar Sunni da ke cikin kwamitin tsara tsarin mulkin kasar suna ganin cewa, darikar Sunni ba ta gamsu da gyare-gyare na karshe ba. Shugaban darikar Sunni a fannin siyasa kuma mataimakin shugaban kasar Ghazi al-Yawar da shugaban majaliar jama'ar kasar Hajem al-Hassani ba su halarci taron da majalisar jama'ar kasar ta shirya a ran nan ba. Bayan da majalisar jama'ar kasar ta rikon kwarya ta amince da wannan shiri, wakilan darikar Sunni sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka ki amincewa da wannan shirin tsarin mulkin kasar.

Masu nazarin harkokin yau da kullum sun yi hasashen cewa, ko da yake bisa abubuwan da aka tanada cikin shari'ar kasar Iraq, ba tilas ba ne majalisar jama'ar wucin gadi ta kasar ta kada kuri'a kan sabon shirin tsarin mulkin kasar, duk da cewa, ya kamata sabon tsarin mulkin kasar ya zama wani tushe ne wajen shimfida dimokuradiyya a kasar Iraq nan gaba. Amma rukunnoni daban daban na kasar Iraq sun sha yin gardama kan aikin tsara sabon tsarin mulkin kasar, ko da kasar Amurka ta matsa lamba, amma a karshe dai ba su sami ra'ayi daya ba. Masu kula da harkokin yau da kullum suna ganin cewa, saboda dalilai daban daban, ko da yake an gabatar da sabon shirin tsarin mulkin kasar a hukunce, amma ya zuwa yanzu ba za a iya tabbatar da makomarsa ba.

Da farko, ba a warware abun da ke fi jawo hankulan darikokin Shi'a da Kurdawa da Sunni, wato tsarin tarayya, a cikin wannan shirin tsarin mulkin kasar ba, wannan ya dasa nakiya a cikin hanyar sake gina tsarin siyasa a kasar Iraq.

Na biyu kuma, bisa abubuwan da aka tanada cikin tsarin mulkin kasar na rikon kwarya, an ce, a cikin kada kuri'ar raba gardama da za a yi a watan Oktoba, idan masu kada kuri'a da yawansu ya kai kashi 2 bisa 3 na larduna guda 3 daga cikin guda 18 gaba daya sun ki amincewa da wannan shiri, to, za a ki amincewa da shirin tsarin mulkin kasar. Yanzu Larabawa masu bin darikar Sunni suna samun rinjaye a cikin larduna guda 4 na kasar. Wakilin da ke cikin kwamitin tsara tsarin mulkin kasar mai bin darikar Sunni Hussein al-Falluji ya yi bayani a ran 28 ga watan nan cewa, darikar Sunni za ta ki amincewa da wannan shiri a cikin kada kuri'ar raba gardama da za a yi. A sa'i daya kuma, wakilai masu bin darikar Shi'a sun ba da wata sanarwa a ran nan cewa, su ma za su ki amincewa da wannan shiri. Idan a ki amincewa da wannan shiri, to, kasar Iraq za ta koma baya kamar yadda take ciki kafin aka yi babban zaben shugaban kasar a watan Janairu na shekarar da muke ciki, za a bata dukan kokarin da aka yi a da.

Bayan da aka yi babban zaben shugaban kasar a watan Janairu, dakarun da ke bin darikar Sunni sun sha tayar da harkokin nuna karfin tuwa, an tsananta halin da kasar Iraq take ciki a fannin tsaron kai, an daina farfado da tattalin arzikin kasar. Idan darikar Sunni ba za ta gamsu da ayyukan siyasa da za a yi a nan gaba ba, to, halin da kasar Iraq take ciki a fannonin tsaron kai da siyasa da farfado da tattalin arzikin kasar zai kara lalacewa, a maimakon kyautatuwa. A cikin irin wannan hali ne, ko da an zartas da sabon tsarin mulkin kasar a cikin kada kuri'ar raba gardama da za a yi, amma da kyar a aiwatar da shi a nan gaba.

Saboda haka ne, ko da yake an gabatar da sabon tsarin mulkin kasar Iraq, amma ba a iya tabbatar da makomarsa ba tukuna. Duk da cewa, kasashen duniya suna fatan dukan rukunnonin kasar Iraq za su dora muhimmanci kan yin hadin kai, za su ci gaba da yin shawarwari da ingiza ayyukan siyasa, ta yadda za a tabbatar da 'yan kasar Iraq da su tafiyar da harkokinsu da kansu.(Tasallah)