Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-26 20:05:21    
An yi kira da a warware matsalar faruwar hadarin mahakar kwal kullum bisa kaida

cri

Ran 25 ga wata a nan birnin Beijing, taro na karo na 17 na kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya saurari rahoto dangane da binciken yadda ake aiwatar da dokar aikin kawo albarka cikin kwanciyar hankali. Rahoton ya gabatar da sakamakon da aka samu a cikin shekaru 3 da suka wuce da ake aiwatar da wannan doka ta yawan kiddidiga dakuma a hakika, kuma ya nuna tsanancewar halin da ake ciki yanzu na kwanciyar hankalin mahakar kwal na kasar Sin, kuma ya gabatar da bukatu da shiri kan ayyukan da abin ya shafa na gwamnati nan gaba. Yanzu, ga cikakken bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana:

Binciken aiwatar da doka shi ne muhimmiyar hanya ta kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa kan aiwatar da ikonsa na sa ido. A ko wace shekara, kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa zai aika da kungiyar bincike zuwa matsayi na yau da kullum don binciken halin aiwatar da wasu muhimman dokoki, bisa muhimman matsalolin da ke jawo hankulan jama'a. A cikin 'yan shekaru masu zuwa, an yi samun aukuwar manyan al'amuran hadariri a a mahaka kwal a kasar Sin, wanda ya kawo hasara sosai ga rayuka da dukiyoyin jama'a, wannan kuma ya jawo hankulan zaman al'umma a fannoni daban daban. Binciken dokar aikin samar da albarkar kasaa a cikin kwanciyar hankali da aka fara yi a karshen watan Afril nashekarar da muke ciki shi ne mai da hankali kan binciken kwanciyar hankali na mahakar kwal.

Rahoton ya nuna cewa, an bayar da dokaraikin samar da albarka a cikin kwanciyar hankali wannan ya alamanta cewa, samar da kayayyaki a cikin kwanciyar hankali ta kasar Sin ta fara bin kan hanyar doka, matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka a jere sun sa yawan al'amarin kwanciyar hankali na aikin samar da albarka da yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya ragu a cikin shekaru 2 da suka wuce. Amma, rahoton ya ce, muhimman matsalolin kwanciyar hankali na mahakar kwal da ake yin bicike suna ta yin tsanani.

Kan maganar dalilan da ke jawo wadannan matsaloli, Mr. Li Tieying, mataimakin shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa, wanda ke shugabancin kungiya don yin bincike kan kwanciyar hankalin mahakar kwal a shiyyoyin siyasa na matsayin jiha na kasar Sin, ya yi bayani a cikin rahoto cewa:

"Dalili na farko shi ne, ayyukan samar da albarkatun a cikin kwanciyar hankali ba su dace da bukatun sabon zamani ba, mahakar kwal da ba na kasa ba suna da yawa, wadanda ba su da cikakken karfin fasaha sun kasa samar da sharadodin da suka wajabta, da kuma ba da ja gora kan fasahohin samar da albarkatun. Na biyu, rashin gudanarwar masana'antu, kuma tsarin sa ido kan kwanciyar hankali bashi da inganci. Na uku, ba a san muhimmancin aikin samar da albarkatu sosai ba cikin kwanciyar hankali, kuma ana yawan rashin bin doka."

Rahoton yana ganin cewa, tilas ne ana kayadde ayyukan samar da albarkatu cikin kwanciyar hankali bisa doka. Mr. Li Tieying ya jaddada cewa,

"Ya kamata a kafa tsarin binciken kwanciyar hankali mai amfani a cikin dogon lokaci, za a juya aikin dudduba da gudanarwa daga mai da hankali kan binciken al'amari zuwa rigakafi da sarrafawa, aiwatar da tsarin cikin kwanciyar hankali sosai, da karfafa ayyukan sa ido da a yau da kullum. A sa'i daya kuma, a bayar da taimakon kungiyar ma'aikata sosai kanbunkasa aikin samar da albarkatu cikin kwanciyar hankali."

Bayan haka kuma, rahoton ya bayyana shiri na farko kan gyare-gyare da bunkasuwar masana'antun kwal na kasar Sin. A cikin rahoton, Mr. Li Tieying ya ce,

"Ya kamata majalisar gudanarwar ta yi nazarin matsalar tsarin gudanarwar masana'antun kwal da ke dacewa da sabon zamani tun da wuri; da kafa manyan sansani da kungiyoyi; da sayar da nazarin muhimman manufofin na kwanciyar hankalin mahakar kwal a cikin shirin bunkasuwar fasaha a cikin dogon lokaci na kasar Sin; da kuma sarrafa da albarkatu sosai, hak kafa halin ayautar da albarkatu cikin ilmin kimiyya, da adalci, da bisa tsari; a sa'i daya kuma akara karfin ba da taimakon kudi, da kyautatta tsarin zuba jari kan kwanciyar hankali." (Bilkisu)