Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-24 20:12:35    
WHO ta mai da hankali a kan maganar lafiya da kasashen Afirka ke fuskanta

cri

A ran 22 ga watan nan, a birnin Maputo, babban birnin kasar Mozambique, an bude taron kwamitin shiyyar Afirka na 55 na kungiyar kiwon lafiya ta kasashen duniya wato WHO. Mutane daruruwa ciki har da ministocin kiwon lafiya da wakilansu na kasashen Afirka, wato kasashen da ke cikin kungiyar WHO da wakilan hukumomin kiwon lafiya na yankuna daban-dabam da ba na gwamnati ba sun halarci wannan taro. Babban direkta na kungiyar kiwon lafiya ta duniya Wook-Jong Lee ya yi kira a gun taron, cewa ya kamata dukkan kasashen duniya su mai da hankulansu a kan maganar lafiya da kasashen Afirka ke fuskanta da kuma ba da goyon bayansu ga mutanen kasashen Afirka domin kyautata halin lafiyar da suke ciki.

Kuma a gun taron nan na kwanaki biyar, wakilai masu halartar taron za su yi tattaunawa kan yin rigakafi da kuma sarrafa ciwon kanjamau da na tibi da na malariya da dai sauran ciwace-ciwace, da yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tsarin aiki na sarrafa taba, da 'yan kwadago da suke aikin kiwon lafiya a shiyyar Afirka da kuma musanyar masu aikin kiwon lafiya a duniya. Yayin da malam Wook-Jong Lee yake jawabi a gun bikin bude taron, ya yi nuni da cewa, a ko wace shekara mutanen Afirka fiye da miliyan su kan mutu sakamakon ciwon kanjamau da na Marburg da na malariya da na huhu da na kwalara da na shan inna da dai sauran ciwace-ciwace, wannan ya taka mumunar rawa ga kokarin da kasashe daban daban na Afirka ke yi domin neman samun bunkasuwa. Kuma domin ba da taimako ga babban yankin Afirka kan rigakafi da kuma warkar da ciwace-ciwace iri iri, Wook-Jong Lee ya bayar da sanarwar cewa, yawan kudin da kungiyar kiwon lafiya ta duniya za ta bayar ga shiyyar Afirka zai karu da kashi 30 cikin kashi dari.

A cikin dogon lokaci, ciwon kanjamau ya yadu sosai a kasashen Afirka, wanda yake barazana sosai ga lafiyar jikin mutanen Afirka. Ban da ciwon kanjamau ba, halin ciwon huhu da na kuturta da na shan inna da dai sauran ciwace-ciwace da kasashen Afirka suke ciki yana da tsanani sosai, bugu da kari kuma yawan yara da mata da suka mutu a shiyya ya fi yawa a duk duniya. Muhimmin dalilin da ya sa mutanen Afirka ba su da lafiyar jiki shi ne sabo da rashin isassun 'yan kwadago da ke aikin kiwon lafiya a shiyyar Afirka da kuma karancin kudi da fasahohi na kiwon lafiya. A wani gefe kuma, yawancin kasashen Afirka suna fama da talauci, shi ya sa da kyar suke iya samar da hidimar jiyya ga marasa lafiya. A sa'i daya kuma, Halin hijirar kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya da kasashen Afrika ke ciki ya yi tsanani sosai, wanda ya yi sanadiyar rashin likitoci a kasahen.

Ra'ayin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, taron ba kawai ya samar da dama ga kasashen Afirka daban daban da su yi cudanya tsakaninsu kan kalubalen da suke fuskantar a wajen maganar kiwon lafiya ba, har ma zai samar da zarafi gare su kan samun kulawa da goyon baya daga kasashen duniya a wajen maganar kiwon lafiya a Afirka. Kuma ana fatan taron zai sa kaimi ga gwamnatocin kasashen Afirka daban daban da kungoyoyin da ba na gwamnati ba da kuma dukkan kasashen duniya da su yi iyakacin kokarinsu wajen warware maganar kiwon lafiya ta kasashen Afirka, ta yadda zai ba da taimako ga cimma 'burin samun bunkasuwa cikin sabon karni' kan rage rabin yawan mutane masu fama da talauci na duk duniya har zuwa shekara ta 2015.(Kande Gao)