A ran 22 ga wata a nan birnin Beijing aka yi wani taron manyan jami'ai a karo na hudu domin tattauna batun hadin kan kasar Sin da Afrika.Wakilan da suka zo daga kasar Sin da sauran kasashe 46 na Afrika da 'yan kallo na kungiyoyin bangarori shida na Afrika da kuma jakadu na kasashen Afrika a Sin sun halarci taron nan.
Wani jami'in gwamnatin Sin wanda ya halarci taron ya bayyana cewa kasar Sin za ta kara bunkasa mu'amala da hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da ciniki. A cikin shekarun baya mu'amala da hadin kai da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na kara kyauttuwa.Jimlar kudin ciniki tsakanin Sin da Afrika ta zarce dalar Amurka biliyan 18 daga watan Janairu zuwa watan Yuni na bana,wato ta karu da kashi 40 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.A sa'I daya kuma shirye-shiryen ciniki tsakanin Sin da Afrika na kara daidaituwa,kayayyakin da Afrika ta fitar da su zuwa kasar Sin sai kara yawa suke,a shekara ta 2004 kasar Sin ta sami gibin kudin da ya kai dalar Amurka biliyan biyu wajen ciniki da kasashen Afrika.
A taron manyan jami'ai a karo na hudu domin tattauna batun hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika da aka fara a ran 22 ga wata,shugaban sashen kula da harkokin Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Xu Jinghu ta bayyana cewa kasar Sin ta tsara manufofi da dama domin bunkasa ciniki dake tsakanin kasar Sin da Afrika.Ta ce" "Ya zuwa karshen watan Mayu na bana,kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin ciniki da kasashe 41 na Afrika,ta daddale yarjejeniyoyi na gudun haraji sau biyu tsakaninta da sauran kasashe 8 na Afrika,ban da wannan kuma ta yafe harajin wasu kayayyakin ciniki na kasashe 28 na Afrika.Tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekara ta 2005,kasashe 25 na Afrika sun cin gajiyar soke harajin ire iren kayayyakin ciniki 190,sauran kasashe uku suna nan suna cika takardun da ya kamata su cika domin cimma burin nan. Kan fannin hadin kai na zuba jari,ya zuwan karshen watan Yuni na bana,jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye zuwa Afrika ya kai dalar Amurka miliyan 750,jarin nan ya shafi kasashe 49 na Afrika kuma ya shafi fannonin ciniki da gyara kayayyaki da sadarwa da sufuri da kuma gyara amfanin gona da sauransu.
Mataimakin shugaban sashen kula da hadin kan tattalin arziki da kasashen waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Mista Zhao Chuang ya bayyana cewa hadin kan kasar Sin da Afrika wajen zuba jari na taimakon juna,ba ma kawai yana taimakawa cigaban masana'antun kasar Sin da kuma tattalin arzikinta,har ma ya ba da taimako wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika.Ya ce cigaban tattalin arzikin Afrika ya kawo dama da yawa na zuba jari ga masana'antun kasar Sin,a nan gaba kasar Sin za ta cigaba da dukufa wajen kara karfin hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika wajen zuba jari.Ya ce"gwamnatin kasar Sin za ta kara sa kaimi ga masana'antunta da su nuna iyawarsu da fiffikonsu da kai kudade da fasahohi da kayayyakin ayautarwa da fasahohin kula da masana'antu ga kasashen Afrika,kasar Sin ta mai da hankalinta wajen zuba jari a fannonin albakartai da aikin gona da saka da manyan ayyuka da sadarwa da kera kayayyakin da ke aiki da wutar lantarki."
Manzon musamman gwamnatin Habasha wanda ya halarci taron Mista Haile-Kiros Gessesse ya bayyana cewa mu'amala da hadin kai da ake yi tsakanin Sin da Afrika sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa Afrika.Ya yi fatan bangarorin biyu za su cigaba da karfafa hadin kansu a wannan fannin da kara bunkasa dangantakar aminci da hadin kai tsakanin Sin da Afrika.Ya ce Yayin da ake kai ga manufar tattalin arziki ta duniya bai daya,hadin kan tattalin arziki ya zama wani muhimmin abu tsakanin kasashe matasa.Kamata ya yi mu mai da dangantakar tattalin arziki da ciniki ta zama muhimmin abu a huldar dake tsakanin Sin da Afrika.Ya kamata Sin da kasashen Afrika su karfafa hadin kansu a wannan fanni domin moriyar mutanen kasashensu.Bisa labarin da muka samo,an ce ban da batun mu'amala da hadin kai a fannin tattalin arziki da ciniki a taron nan,wakilan mahalartan taron za su tattauna mu'amala da hadin kai da ake yi tsakanin Sin da Afrika wajen siyasa da al'adu da kimiyya da ilimi da sauransu.(Ali)
|