
A ran 22 ga wata, lokacin da yake ganawa da kungiyar wakilan kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ta jam'iyyar the People first Party ta Taiwan, jagoran ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya ce, bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyinsu kan yadda za a shirya taron tattaunawa da za a yi a tsakanin manyan jami'an jam'iyyun siyasu biyu a watan Satumba a birnin Shanghai.
A watan Mayu na shekarar nan, shugaba James CY Soong na jam'iyyar the People first Party ya kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara, inda ya yi shawarwari da Mr. Hu Jintao, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya kan yadda za a farfado da yin shawarwari a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin halin zaman daidai wa daida bisa ka'idojin Sin daya tak da suke bi tare da kiyewar yunkurin 'yancin kan Taiwan. Shirya taron tattaunawa a tsakanin manyan jami'an jam'iyyun siyasu 2 wani muhimmin mataki ne da suka dauka domin amincewa da ra'ayi daya da suka samu. (Sanusi Chen)
|