
A ran 19 ga wata a nan birnin Beijing, hukumar gandun daji ta kasar Sin ta bayar da ma'aunar zaben Panda da za a samar wa lardin Taiwan kamar abin kyauta.
A gun wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, jami'ai da masana na babban yankin kasar Sin sun ce, wannan ma'auna ta hada da yawan shekaru haihuwa da halin lafiya da suke ciki da halayensu da dai sauransu.
Mr. Cao Qingrao, kakakin hukumar gandun daji ta kasar Sin ya ce, bangaren babban yankin zai tabbatar da zaban kyawawan Panda namiji daya da mace daya wadanda suke da lafiya kwarai. A sa'i daya, ya bayyana cewa, bangaren babban yankin kasar Sin yana fatan za a isar da Panda 2 a Taiwan tun da wuri domin cimmma burin ganin Panda da mutanen Taiwan suke nema. (Sanusi Chen)
|