Jama'a masu karatu, A kwanan baya, Mr. Alpha Oumar Konare, shugaban kwamitin Tarayyar Afirka wanda ke yin ziyara a nan kasar Sin, ya ce, "bunkasuwa da karfi da kasar Sin, wato tsohuwar aminiya ce ga Afirka, ta samu wata kyakyawar dama ce ga Afirka. Mr. Konare ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da wakilan kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin.
Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Sin ta yi masa ne, a ran 14 ga wata da safe Mr. Konare ya iso nan birnin Beijing ya fara ziyararsa ta aiki ta kwanaki 5 a nan kasar Sin. Wannan ne karo na 3 da Mr. Konare, wato tsohon shugaban kasar Mali ya kawo wa kasar Sin ziyara a cikin shekaru 13 da suka wuce. Mr. Konare ya kara da cewa, "Da idona ne ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasuwar tattalin arziki. A kowane lokacin da na yi ziyara a kasar Sin, na ga kasar Sin tana da nagartaccen karfi domin zaman daidai da halin da ake ciki a duniya."
A cikin shekaru 26 da suka wuce, wato tun daga shekarar 1979 zuwa shekarar 2004, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 9.4 cikin kashi dari a kowace shekara. Amma Mr. Konare ya ce, lokacin da kasar Sin take bunkasa tattalin arzikinta, ta kan mai da hankali kan yadda za ta ba da gudummawa ga bunkasuwar Afirka, kuma tana sauraran ra'ayoyin kasashen Afirka game da harkokin duniya. Lokacin da kasashen Afirka suke neman 'yanci kan al'umma da yin gwagwarmaya da wariyar kabilu da neman bunkasuwar tattalin arzikinsu, kasar Sin ta nuna musu goyon baya kwarai. Bugu da kari kuma, kasar Sin ta kan nuna goyon baya ga Afirka har kullum lokacin da ake daidaita harkokin duniya.
Sannan kuma, Mr. Konare ya ce, "A idona, kasar Sin kasa ce da take mallakar sa'a, kuma take iya daidaita matsalolin da ke gabanta da kanta. Haka nan kuma, kasar Sin aminiya ce ta Afirka har abada."
Bisa kididdigar da aka yi, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, saurin cinikayya da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya yi sama kwarai. A shekarar 2000, jimlar kudaden cinikin waje da aka yi a tsakaninsu ta kai dalar Amurka wajen biliyan 10.8, amma a shekarar 2004, wannan adadi ya kai dalar Amurka biliyan 30.
Mr. Konare ya ce, kasar Sin tana dogara da kanta domin neman bunkasuwa. Kasashen Afirka suna fatan za su iya dogara da kansu kan yadda za su iya daidaita matsalolin da ke kasancewa a gabansu. "Muna fatan Afirka ba ma kawai wata kasuwa ba, har ma za ta iya kera da sayar da kayayyakin da za su kera da kansu", in ji Konare.
Bugu da kari kuma, Mr. Konare yana fatan za a iya kara yin hadin guiwa a tsakanin Afirka da kasar Sin. Ya ce, Afirka tana da muhimmin matsayi bisa manyan tsare-tsare. Idan dukkan kasashe 53 na Afirka sun gama kansu, wannan wani muhimmin karfi ne. Yanzu kasashen Afirka da kasar Sin suna fuskantar nauyi daya, wato kiyaye mulkin kai kan siyasa kuma da neman bunkasuwar tattalin arziki da aka dora musu. Sabo da haka, Afirka da kasar Sin za su iya kafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu.
Sannan kuma, Mr. Konare yana fatan bangarorin biyu za su iya kafa tsarin yin shawarwari kan harkokin siyasa a tsakanin manyan jami'ansu a gun taron dandalin hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Sabo da haka, bangarorin biyu za su iya kara tattaunawa da tsara shirin neman bunkasuwa, kuma za su iya kafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. (Sanusi Chen)
|