Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-16 19:57:20    
Rukunin addinai na Sin ya ba da sanarwa don tunawa da cikon shekaru 60 da jama'ar Sin suka ci nasarar yakin kin mahara Japanawa

cri

Domin tunawa da cikon shekaru 60 da jama'ar kasar Sin suka ci nasarar yakin kin mahara Japanawa da kuma cin nasarar yakin kin fascist a duniya, kwamitin zaman lafiya na rukunin addinai na kasar Sin ya kira taron tattaunawa a ran 14 ga watan nan a nan birnin Beijing da kuma bayar da sanarwar zaman lafiya ta rukunin addinai na kasar Sin, inda aka bayyana cewa, kawar da sanadin yaki da kuma kiyaye zaman lafiya na duniya a bayyane aiki ne na masu bin addinai. Kamata ya yi dukkan addinai daban daban su hada kai domin yin kokari tare kan kiyaye zaman lafiyar dan Adam. Yanzu ga cikakken labarin da wakilinmu ya aiko mana.
Dukkan masu halartar taron suna ganin cewa, yakin kin fascist na duniya yakin adalci ne a cikin tarihin dan Adam, kuma yakin kin harin mahara Japanawa domin neman 'yancin kai da jama'ar Sin suka yi wanda shi ne wani muhimmin kashi na yakin kin fascist na duniya.
Mataimakin shugaban kungiyar addinin Budda ta kasar Sin Sheng Hui ya yi nuni a cikin jawabinsa, cewa"shekarar da muke ciki shekara ce cikon shekaru 60 da jama'ar kasar Sin suka ci nasarar yakin kin mahara Japanawa da kuma aka ci nasarar yakin kin fascist a duniya, yin waiwaye da tuba kan tarihi na wancan lokaci yana da ma'ana mai muhimmanci ga karfafa ra'ayin kishin kasa, da sa kaimi ga hadin kai da ke tsakanin kabilu daban daban da kuma addinai daban daban, da kiyaye zaman karko na kasa, da karfafa zumunta tsakanin jama'ar kasashe daban daban, da kuma kiyaye zaman lafiya na duk duniya."
Yau da shekaru 60 da suka gabata ne, jama'ar kasar Sin suka ci nasarar yakin kin mahara Japanawa bayan da suka yi matukar gwagwarmaya, kuma sun yi babbar hasara a cikin yakin, yawan fararen hula da sojoji da suka mutu da kuma jin rauni ya zarce miliyan 35, kuma yawan kudi da kayayyakin da aka kashe a cikin yakin ya kai fiye da dala biliyan 560. shugaban kungiyar addinin Musulmi ta kasar Sin Chen Guangyuan yana ganin cewa, bai kamata a kauce wa abubuwan da aka aikata a tarihin ba, kuma ya bayyana cewa"gwamnatin Japan ta yi watsi da kin amincewar kafofin watsa labarai na duniya da abin da ake ji a zukatan jama'ar Sin, kuma kusoshinta sun ziyarci Haikalin Yasukuni da kuma yin gyare gyare kan littattafan koyarwa ba tare da jin tsoron kome ba domin neman kawar da laifuffukan da mahara Japanawa suka yi da kuma farfado da nuna karfin soja na Japan, ko shakka babu wannan zai haddasa suka mai tsanani da dukkan jama'ar Sin da mutanen duniya masu son zaman lafiya za su yi."
Kuma a gun taron, shugaban kwamitin zaman lafiya na rukunin addinai na kasar Sin kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Ding Guangxun ya karanta sanarwar zaman lafiya ta rukunin addinai na kasar Sin,"neman zaman lafiya buri ne na dukkan addinai, shi ya sa ya kamata addinai daban bana su raya abubuwa masu kyau domin karfafa yin tattaunwa tsakaninsu da kuma fahimtar juna a tushen zaman daidai wa daida da jin tausayin jama'a da girmama wa juna da kuma yin hakuri. Ko shakka babu karfafa hadin kai da jituwa da ke tsakaninsu za su taka muhimmiyar rawa ga zaman lafiyar duniya. Za su shiga harkokin zaman lafiya da dukkan kungiyoyin addinai na kasashen duniya masu aminci suka shirya da kuma goyon bayan kudurori masu ba da taimako ga zaman lafiya. Ban da wannan kuma za mu tsamo darasi daga tarihi domin fuskantar abubuwan da za su wakana a nan gaba, da kuma yin kokari cikin dogon lokaci domin kafa wani sabon tsarin zamantakewar al'umma na zaman lafiyar dan Adam."(Kande Gao)