Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-11 17:32:00    
Kasar Mauritania da kasashen waje da ita sun dan canja ra'ayoyinsu game da gwamnatin mulkin sojan kasar

cri
Tawagar wakilan ministoci da Kawancen Kasashen Afirka wato AU ya tura ta sauka birnin Nouakchott, hedkwatar kasar Mauritania a ran 9 ga watan nan, inda suka yi shawarwari da kwamitin soja na dimokuradiyya da adalci da ya yi juyin mulki a kan maido da odar tsarin mulkin kasar. Wannan ne karo na farko da tawagar koli ta kungiyar AU da gwamnatin mulkin soja ta kasar Mauritania suka tuntubi juna, bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasar, kuma suka hambarar da gwamnatin Taya.

Alamu daban daban sun nuna cewa, 'yan kasar Mauritania da mutanen kasashen waje sun fara canja ra'ayoyinsu kadan game da gwamnatin mulkin soja ta kasar Mauritania.

Da farko, kungiyar AU da Kawancen Kasashen Larabawa sun canja ra'ayoyinsu game da gwamnatin mulkin soja ta kasar Mauritania a bayyane.

Ran 3 ga wannan wata, sojojin wadanda rundunar sojan tsaron lafiyar shugaban kasar da hukumar tsaron kasar suka zama ginshikinsu sun yi juyin mulki sun hambarar da gwamnatin Taya, saboba shugaba Taya ba ya gida. A lokacin nan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar AU da sauran kungiyoyin kasa da kasa sun la'anci wannan juyin mulkin soja bi da bi, sun bukaci a maido da tsarin mulkin kasa da oda a kasar nan da nan. Kwamitin zaman lafiya da tsaron kai na kungiyar AU shi ma ya tsai da kudurin musamman a ran 4 ga watan nan, inda ya dakatar da kasar Mauritania daga cikin mambobinta. Duk da cewa, bayan kwanaki 6 kawai da aka yi juyin mulki, kungiyar AU ta aika da tawagar ministoci zuwa birnin Nouakchott, inda ta yi shawarwari da shugabannin gwamnatin mulkin soja. Ran 9 ga watan nan, Mohammed Abdel-Rahman-Shalgam, ministan harkokin waje na kasar Libya ya kuma yi shawarwari da shugabannin gwamnatin mulkin sojan. Bisa labarin da aka bayar, an ce, Kawancen Kasashen Larabawa zai aika da wata tawagar wakilai zuwa birnin Nouakchott nan gaba kadan ba da dadewa ba. Lokacin da yake zantawa da manema labaru a ran 9 ga watan nan a Nouakchott, jakadan kasar Afirka ta Kudu da ke kasar Mauritania Rantobeng William Mokou ya bayyana cewa, kungiyar AU ta ki amincewa da juyin mulkin soja, amma mai yiwuwa ne matsayin da take tsayawa a kai bai dace da halin da dukan kasashe mambobin kungiyar suke ciki ba.

Na biyu, kasar Amurka da Kawancen Kasashen Turai suna goyon bayan kungiyar AU da ta aika da tawagarta zuwa Mauritania don yin shawarwari da shugabannin gwamnatin mulkin soja.

Bayan da aka yi juyin mulkin soja a kasar Mauritania, kakakin wucin gadi na ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka George Casey ya taba bayyana cewa, kasar Amurka za ta yi kokari tare da kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kungiyoyin duniya don maido da odar tsarin mulkin kasar da kuma gwamnatin shugaba Taya a kasar tun da wuri. Amma bayan da aka labarta cewa, tawagar wakilan kungiyar AU da shugabannin gwamnatin mulkin soja ta Mauritania sun yi shawarwari, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta yi bayani a bayyane a ran 8 ga watan nan cewa, tana goyon bayan ziyarar da tawagar kungiyar AU ta yi, sa'an nan kuma, za ta yi watsi da maganar maido da gwamnatin Taya. Wani jami'in jakadanci na kungiyar EU da ke birnin Nouakchott ya kuma bayyana cewa, idan gwamnatin mulkin soja ta kasar Mauritania ta cika alkawarinta, za ta sake yin zaben dimokuradiyya a cikin shekaru 2 masu zuwa, to, watakila kasashen duniya za su amince da gwamnatin mulkin soja ta kasar ta yanzu.

Na uku, halin da kasar Mauratania take ciki a yanzu yana amfana wa gwamnatin mulkin soja. Saboda bayan da ta yi juyin mulki, gwamnatin mulkin soja ta sarrafa halin da birnin Nouakchott take ciki cikin sauri, ta kuma dauki matakai da dama don kara saurin kafa gwamnatin rikon kwarya, ban da wannan kuma, ta yi alkawarin cewa, za a sake yin babban zaben gama gari a cikin shekaru 2 masu zuwa da kuma kada shugabannin gwamnatin mulkin soja da firaministan gwamnatin rikon kwarya su shiga babban zaben shugaban kasar, farar hula masu yawa na kasar suna nuna goyon bayansu da kuma maraba da wannan. Yanzu wasu jakadun da ke kasar Mauritania sun yi bayani a wurare daban daban cewa, ya kamata kasashen duniya su girmama buri da zabin da al'ummar kasar Mauritania suka yi.

Bayan da ya yi shawarwari da shugaban kwamitin soja na dimokuradiyya da adalci na Mauritania Ely Ould Mohamed Vall a ran 9 ga wannan wata, ministan harkokin waje na kasar Libya Mohammed Abdel-Rahman-Shalgam ya ce, a ganinsa, al'ummar kasar Mauritania sun riga sun amince da kwace mulkin kasar da aka yi, saboda haka ya kamata gamayyar kasashen duniya ta girmama zabin da al'ummar kasar Mauritania suka yi.

A sa'i daya kuma, shugaba Taya da ya taba zama a kasar Nijer a sakamakon juyin mulkin soja ya tashi zuwa kasar Gambiya a ran 9 ga watan nan don neman mafakar siyasa, saboda babu wanda yake sha'awar kirar da ya yi ta komawa gida da kuma sake karbar ragamar mulkin kasarsa.(Tasallah)