Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-10 16:42:12    
Wasannin Olympics da za a shirya a shekarar 2008 zai samar da damar ciniki a Beijing

cri

A 'yan kwanakin baya, mataimakiyar shugaban hukumar kula da yawon shakatawa ta Beijing Madam Xiong Yumei ta bayyana cewa, yayin da wasannin Olympics na shekarar 2008 ke kara kusantawa, birnin Beijing zai kara daukar hankulan duk duniya, sakamakon haka, ko shakka babu, wasannin Olympics da za a shirya a shekarar 2008 zai kara samar wa aikin yawon shakatawa na Beijing babbar damar ciniki. Xiong Yumei ta ce, daga yanzu zuwa shekarar 2008, birnin Beijing zai kara karfinsa wajen inganta manyan ayyukan yawon shakatawa, a sa'i daya kuma, zai karfafa kwarewar bautawa ta masu aiki a fannin yawon shakatawa tare da kago wani kyakkyawan muhalli ga 'yan yawon shakatawa na ciki da waje.

Birnin Beijing ya kasance cibiyar siyasa da ta al'adu da kuma ta yin mu'amala da sauran kasashen duniya, haka kuma birni ne mai dogon tarihi tare da al'adu, yana da wurare masu ban sha'awa masu yawan gaske, sabili da haka, birnin Beijing ya jawo hankulan 'yan yawon shakatawa ciki da waje da yawa a ko wace shekara. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a shekarar 2004, 'yan yawon shakatawa na kasashen waje da yawansu ya zarce miliyan 3 sun zo nan birnin Beijing domin yawo, yawan 'yan yawon shakatawa da suka zo daga sauran wuraren kasar Sin ya kai miliyan 100, a sakamakon haka, birnin Beijing ya sami kudin shiga da yawansu ya zarce kudin Sin biliyan 130 a kan sha'anin yawon shakatawa.

Za a shirya wasannin Olympics na shekarar 2008 a birnin Beijing, to, wannan ya samar wa aikin yawon shakatawa a birnin Beijing babbar damar ciniki. Mataimakiyar shugaban hukumar kula da yawon shakatawa ta Beijing Madam Xiong Yumei ta bayyana cewa,

'Hukumar kula da yawon shakatawa ta Beijing ta yi hasashen cewa, daga shekarar 2005 zuwa shekara ta 2007, yawan 'yan yawon shakatawa da za su zo daga kasashen waje zai karu daga kashi 7 zuwa 8 bisa dari, a shekarar 2008, zai karu da 13%. Domin haka, birnin Beijing zai karbi 'yan yawon shakatawa na kasashen waje miliyan 4 da dubu 400, 'yan yawon shakatawa na kasar Sin za su kai miliyan 150.'

Wannan jami'a ta kara da cewa, domin yin amfani da damar ciniki da wasannin Olympics zai samar wa Beijing da kago wani kyakkyawan muhalli ga 'yan yawon shakatawa ciki da waje, birnin Beijing yana kyautata matsalolin da ke kasancewa a fannin yawon shakatawa. Ta ce, ko da yake sha'anin yawon shakatawa na Beijing yana bunkasuwa sosai, amma bai fi biranen yawon shakatawa na kasashe masu sukuni ba. Sabo da haka ne, mataimakiyar shugaban hukumar kula da yawon shakatawa ta Beijing Madam Xiong Yumei ta bayyana cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa wato daga bana zuwa shekarar 2008, birnin Beijing zai kara kokarinsa wajen inganta manyan ayyukan yawon shakatawa, tare da kara kwarewar masu aikin hidima a fannin yawon shakatawa. Ta ce,

'Birnin Beijing zai yi kokari sosai wajen inganta ayyukan hotel da na wuraren yawon shakatawa. A fannin hotel, a halin yanzu dai birnin Beijing yana da hotel da yawansu ya kai 630, amma Beijing ya yi alkawarin cewa, zai samar da hotel da yawansu ya kai 800 a shekarar 2008. za mu kyautata da sabunta hotel da muke da su a yanzu domin makasudin nan.'

Ta ce, domin kyautata muhallin wuraren yawon shakatawa, a farkon rabin shekarar da muke ciki, birnin Beijing ya riga ya zuba jari na kudin Sin da yawansu ya zarce miliyan 50 wajen gina hanyoyin wuraren yawo da kyautata muhalli da kuma kiyaye muhallin abubuwan halitta masu rai ko marasa rai da dai sauransu. A sa'i daya kuma, mun riga mun yi gyare-gyaren wuraren sayar da tikiti da kantuna da dakunan cin abinci da dai sauransu.

Ban da wadannan kuma, birnin Beijing yana ta yin kokari wajen kara kwarewar masu aikin hidima a fannin yawon shakatawa. Bisa labarin da muka samu, an ce, Beijing zai kafa wata cibiyar watsa labaran yawon shakatawa, wadda ke daukar nauyin bayar da labaran yawon shakatawa da sayar da tikiti da karbar 'yan yawon shakatawa da sufuri da dai sauransu, wannan cibiya za ta bayar da gudumowarta wajen wuraren cin abinci da wuraren kwana da tafiye tafiye da ba da jagorancin yawon shakatawa da sayen kayayyaki da nishadi da dai sauran fannoni. Hukumar kula da yawon shakatawa ta birnin Beijing ta yi shirin horar da musu aikin yawon shakatawa a cikin shekaru uku masu zuwa domin kara karfafa kwarewar bautawarsu da iya magana da harsunan waje, ta yadda za a karafafa kwarewar masu aikin a birnin Beijing.(Danladi)