
Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran 9 ga watan nan da muke ciki, a cibiyar bincike aikin kiyaye panda ta kasar Sin dake lardin Sichuan, an fara tafiyar da aikin zaba panda guda biyu masu kyau ta yadda babban yankin kasar Sin zai mika wa yankin Taiwan.
Shugaban ofishin kiyaye panda ya gaya wa maneman labaru cewa, kungiyar kwararru na sassan kula da panda za ta zabi panda guda biyu masu kyau sosai, kana kuma za a yi la'akari kan tsawon haihuwarsu da lafiyar jikinsu da surarsu da sauran sharudansu.
Ban da haka kuma, za a yi la'akari kan dangantakar 'yan iyalansu wato za a zabi panda namiji daya da panda mace daya don kafa sabon iyali daya mai kyau.(Dije)
|