Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-04 14:48:34    
Kasar Sin ta gabatar da sharuda masu sauki ga masana'antun kasar da su zuba jari a kasashen ketare

cri
Kwanan baya a nan birnin Beijing, Mr. Li Dongrong, mataimakin shugabaan hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin ya bayyana cewa, cikin shekaru 2 da 'yan watanni da suka wuce na bayan kasar Sin ta fara yin gyare-gyaren dabarun kula da kudin musanya da aka zuba a kasashen ketare, an sami sakamako mai yakini, kuma an nuna babban goyon baya ga masana'antun kasar Sin wajen kudin musanya da su zuba jari a kasashen ketare. Yanzu, ana nan ana tafiyar da wannan aiki a duk fadin kasar. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.

Daga shekarar 2002 ne kasar Sin ta fara yin jarrabawa wajen gyare-gyaren dabarun kula da kudin musanya da masanaa'natun kasar suka zuba a kasashen ketare. Kafin wannan kuma sabo da karancin ajiyewar kudin musanya, shi ya sa kasar Sin ta tsai da matakai masu tsanani domin kula da kudin musanyar da masana'antun kasar suka yi amfani da su don zuba jari a kasashen ketare, kuma dole ne masana'antun su dawo da jarin da suka samu daga kasashen waje cikin kasar, kada su ci gaba da zuba wannan jari a kasashen ketare domin kara samun bunkasuwa.

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa karuwar aikace- aikacen da masana'antun kasar Sin ke yi wajen zuba jari a kasashen ketare, kuma yawan jarin da suke zuba sai kara karuwa suke, har ma sukan bi wasu sabbin hanyoyi wajen zuba jari wato sun sayi kamfanonin kasashen ketare ko kuma sun sayi hannun jarinsu, sabo da haka tsarin da aka tsara a da bai ishe mu ba wajen kula da kudin musanyar da masana'antun kasar suka yi amfani da su don zuba jari a kasashen ketare. A albarkacin haka ne daga shekarar 2002, kasar Sin ta fara yin gyare-gyare ga wannan aiki.

Mr. Li Dongrong, mataimakin shugabaan hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin ya ce, "Bisa ci gaban da kasar Sin ta samu wajen tattalin arzaiki, yawan kudin musanyar da ta ajiye ya karu, yanzu muna yin gyare- gyare ga irin ayyukan da muka yi a da. A takaice dai, masana'antun kasar Sin ba za su gamu da wahaloli da yawa kamar yadda suka yi a da ba wajen sayen kudin musanya domin zuba jari a kasashen ketare, wato sun sami sauki sosai ga yin wannan aiki".

Wannan aikin gyare-gyare ya samu maraba daga wajen masana'antu da gwamnatocin wurare daban-daban. Kwanan baya ba da dadewa ba, kasar Sin ta fara yin wannan aiki a duk fadin kasar baki daya, kuma an kara yawan kudin musanyar da kowace jihar za ta saya sosai domin zuba jari a kasashen ketare. Mr. Li Dongrong, mataimakin shugabaan hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin ya bayyana ce, ban da cewar kasar Sin ta sassauta tsarin da aka tsayar kan masana'antun kasar kan jarin da suka zuba a kasashen ketare, kuma hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin za ta nuna goyon bayan ga masana'antun kasar da su ci gaba da sayen kudin musanya domin zuba jari a kasashen waje. Ya ce, "Hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin tana da alhaki a wannan fanni wato ta kara samar wa masana'antun kasa da muhalli mai kyau don su zuba jari a kasashen ketare. Yanzu, wani aikin da take yi shi ne saukaka hanyoyin da ake bi domin samar da kudi, wani aiki daban kuma shi ne kara yawan kudin da aka samar domin zuba jari. Ban da wannan kuma, mun riga mun yarda da bankin kasar da bankin masana'antu da kasuwancin kasar Sin da su yi gwaje-gwaje ga yin wannan aiki, wato an yarda da reshen wadannan bankuna da ke kasashen ketare da su nuna goyon baya ga samar da kudi ga masana'antun kasar Sin da ke can kai tsaya". (Umaru)