
A ran 1 ga watan Agusta shugaba El Bashir na kasar Sudan ya bayar da sanarwa cewa, ko da ya ke John Garang, mataimakin shugaba na farko kuma shugaban gwamnatin kudanci na kasar Sudan ya mutu sabo da hatsarin jirgin sama, amma gwamnatin Sudan ta niyyata za ta ci gaba da aikin shimfida zaman lafiya a cikin gidan kasar Sudan.
Garang shi ne mai kafa kungiyar neman 'yancin jama'ar Sudan wadda ita ce babbar kungiyar siyasa a kudancin kasar Sudan. Wannan kungiya kuwa ginshiki ne na kungiyar dakaru 'yan tawaye a kudancin kasar Sudan. Aikace aikacenta na neman hambarar da gwamnati sun ta da yakin basasa na biyu, har mutane fiye da miliyan 2 sun rasa rayukansu, mutane fiye da miliyan 4 sun zama 'yan gudun hijira. Bisa cudanyar da kasashen duniya suka yi ne kudanci da arewaci na kasar Sudan sun fara yin shawarwari a shekara ta 1990. A watan Janairu na bana Garang da shugaba Bashir na kasar Sudan sun sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, sun sa aya ga yakin basasa da aka yi har shekaru 21. Bisa wannan yarjejeniya, Garang ya zama mataimakin shugaba na farko na kasar Sudan a ran 9 ga watan nan.
A ran 30 ga watan Yuli, Garang ya kai ziyarar kansa a Uganda, a kan hanyarsa ta koma gida a ran 31 ga watan nan ne mugun yanayi ya sa jirgin samansa ya fadi, shi da mabiyansa duk sun mutu.
Bayan da aka bayar da labarin mutuwar Garang, an yi tashin hankali a titunan Kartum. Samari 'yan kudanci sun yi fada da 'yan sanda, kuma sun farfasa kantuna da motoci don nuna fushinsu. 'yan sanda sun ce, a cikin tashin hankalin nan an yi hasarar rayuka fiye da 20. gwamnatin Sudan ta dauki matakai don kiyaye zaman lafiya. A kan tituna duk 'yan sanda ne. gwamnatin Sudan kuma ta kafa dokar hana fita da dare.
A sa'I daya kuma shugaba Bashir ya kira taron gaggawa na gwmnati, inda ya yi fatan, kungiyar neman 'yancin jama'ar Sudan za ta zabi magajin Garang tun da wuri don ya kama mukamin mataimakin shugaba na farko na Sudan.
Bayan da Garang ya mutu ba zato ba tsammani, kungiyar neman 'yancin jama'ar Sudan ma ta dauki matakan gaggawa. A ran 1 ga watan nan wannan kungiya ta bayar da sanarwa don tabbatar da cewa, Garang ya mutu a cikin hatsarin jirgin sama sabo da mugun yanayi amma ba sabo da sauran dalilai ba ne. sanarwar nan ta yi kira ga jama'a kada su amaince da jita jita, su yi hakuri don ba da taimako ga kasa da ta wuce lokacin wuya. Kuma ta nuna cewa, wannan kungiya za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da ta kulla da gwamnatin Sudan a watan Janairu na bana.
An bayyana cewa, mutuwar Garang ta zama jarrabawa mai tsanani ga aikin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan, ra'ayi mai amfani da gwamnatin kasar Sudan da kungiyar neman 'yancin jama'ar Sudan suka nuna yana da muhimmancin gaske. Wannan ya sake shaida cewa, bangarorin biyu sun niyyata za su ci gaba da sa kaimi ga aikin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan. (Dogonyaro)
|