Alkaluma na nuna cewa, a watan Yuli da ya gabata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a tsakanin birnin Xiamen na babban yankin kasar Sin da birnin Jinmen na yankin Taiwan na kasar Sin ta jirgin ruwa ya kai dubu 50, wato ya karu da kashi 16.2 a cikin dari idan a kwatanta da shi da na shekarar da ta wuce. Wannan jimla ta kai matsayin koli tun daga aka fara yin zirga-zirga a tsakanin birane biyu a watan Janairu na shekarar 2001.
Bisa labarin da muka samu, an ce, dalilin da ya sa aka samu irin wannan karuwar yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a tsakanin biranen 2, shi ne domin mutanen yankin Taiwan da suka zo babban yankin kasar Sin don yin yawon shakatawa ko shiga wasannin motsa jiki, ko kuma domin yin mu'amala a wajen fannin al'adu sun karu sosai. (Bello)
|