
Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga ma'aikatar tsaron lafiyar zaman al'umma na kasar Sin, an ce tun daga ran 25 ga wata, za a saukake matakan shiga da fita daga babban yankin kasar Sin domin mazaunan yankin Taiwan.
Wani jami'in ma'aikatar ya bayyana cewa, za a hada da matakan shiga da fici da matakin neman izinin zama a babban yankin. Ban da wannan kuma, an yi gyare-gyare kan hanyar duba takardun neman izinin shiga da fici da zama da mazaunan yankin Taiwan za su gabatar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, daga farko, mazaunan yankin Taiwan na kasar Sin sun zo nan babban yankin kasar Sin domin kai wa iyalansu ziyara ko yawon shakatawa kawai, amma yanzu, sun zo nan ne domin zuba jari da yin ciniki da yin karatu da neman aikin yi da yin musanye-musanye a fannonin koyarwa da kimiyya da fasaha da al'adu da kiwon lafiya da wasannin motsa jiki da dai sauransu. A cikin farkon rabin shekarar nan kawai, mazaunan yankin Taiwan wadanda suka shigo babban yankin kasar Sin sun wuce miliyan 2. (Sanusi Chen)
|