A ran 20 ga wata, wakilan darikar Sunni na musulmi na kwamitin mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki sun sanar da cewa cikin gaggawa, sun dakatar da halartar aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar. A ran nan kuma, wakilan darikar Sunni na musulmi da yawansu ya kai hudu sun sanar da janyen jikinsu daga kwamitin. Bisa labarin da muka samu, an ce, 'yan darikar Sunni na musulmi da ke cikin kwamitin mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki za su shirya wani taro a ran 21 ga wata inda suka yanke shawarar ko za su ci gaba da yin aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar Iraki ko a'a.
Dalilin da ya sa 'yan darikar Sunni na musulmi suka dauki matakan nan shi ne domin aka kalubalanci zaman lafiyarsu. A watan da ya gabata, bayan da kwamitin mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki ya yarda da kara wakilan larabawa 'yan darikar Sunni da yawansu ya kai 15 da masu ba da shawara na darikar Sunni 10, sai dakaru sun fara shirin kai su farmaki. Sau da yawa ne kungiyar dakarun da shugaba na uku na kungiyar "Al-Qaida" Abu Musab al-Zarqawi ke shugabanta suka kalubalanci cewa, za su kai farmaki sosai ga 'yan darikar Sunni wadanda suka shiga cikin aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar Iraki. A ran 19 ga wata a birnin Bagadaza, an kashe 'yan darikar Sunni na kwamitin mai hula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki da yawansu ya kai 3.
Wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum sun bayyana cewa, yunkurin tsara shirin tsarin mulki a kasar Iraki yana cikin wani muhimmin wa'adi, amma 'yan darikar Sunni na kwamitin mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki sun datakar da aikinsu ko janye jikinsu daga kwamitin domin yin la'akarin zaman lafiyar kansu, to wannan zai ba da mugun tasiri ga wakilcin da kwamiti mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki da ke da shi, sabo da haka ne, yunkurin tsara shirin tsarin mulkin kasar ya shiga cikin wani mawuyacin hali har ba a sani ba ko za a iya kawo kashen aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar a tsakiyar watan Augusta na bana bisa shiri ko a'a.
Da farko dai, ba mai yiwuwa ba ne babu wakilan larabawa 'yan darikar Sunni a cikin kwamiti mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki. Yawan larabawa 'yan darikar Sunni ya kai kashi 20 cikin dari na jimlar mutanen kasar Iraki, musamman a jihohi hudu da ke yamma maso tsakiyar kasar, yawansu ya sami rinjaye, sabo da haka ne halartar 'yan darikar Sunni cikin kwamitin ta zama wata muhimmiyar alama ga aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar, idan babu kasancewar 'yan darikar Sunni a cikin kwamitin, to, ba za a iya zartas tsarin mulkin kasa da aka tsara ba a gun jefa kuri'ar raba gardama.
Na biyu, an riga an kusan gama aikin tsara shirin tsarin mulkin kasar Iraki, wato bisa ga dukkan alamu yanzu aski ya kai gaban goshi. Shugaban kasar Iraki Talabani ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, idan aka iya daddale yarjejeniya da musulmai 'yan darikar Sunni, to, ana iya sanya ran alheri cewa, za a kawo karshen aikin tsara shirin tsarin mulkin kasa na dogon lokaci a karshen watan Yuli na shekarar da muke ciki. Amma a halin yanzu dai, 'yan darikar Sunni da na Shi'a da Kurdawa suna da bambancin ra'ayoyi masu yawan gaske.
Na uku, shigar 'yan darikar Sunni cikin yunkurin siyasa ta iya hana dakarun da 'yan darikar Sunni ke shugabanta da su dauki matakan soja. Idan 'yan darikar Sunni na musulmi sun dakatar da halartar aikin tsara tsarin shirin mulkin kasa ko sun janye jikinsu daga kwamiti mai kula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki, to, wannan ya sa dakarun 'yan darikar Sunni wadanda ba su ga maciji da gwamnati da kuma kasar Amurka ba za su kara haddasar gurbataccen halin da ake cikin a kasar Iraki, wanda ya zama mahani ga yunkurin sake gina siyasa a kasar da samun zaman laifyarta, abin kara zafi shi ne, mai yiwuwa wannan zai haddasa yakin basasa da ke tsakanin 'yan rukunin Sunni da na Shi'a da kuma Kurdawa.
Bayan da aka kashe 'yan darikar Sunni na kwamitin mai hula da harkokin tsara shirin tsarin mulki na kasar Iraki da yawansu ya kai 3, 'yan siyasa na rukunin Sunni da na Shi'a da dai sauransu sun yi Allah wadai da wannan al'amarin. A sa'i daya kuma, sun ce, wannan aikin da aka yi ba zai iya hana aniyar 'yan darikar Sunni wajen shigarsu cikin yunkurin siyasa ba. Amma ba za a iya sanya ran alheri ga al'amarin ba. Hadin kai da ke tsakanin musulmai 'yan darikar Sunni na da na Shi'a da kuma Kurdawa ya zama tilas ga gudanarwa da aikin tsarin shirin mulkin kasar Iraki lami lafiya.(Danladi)
|