Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-07-20 16:54:37    
An yi kira ga hukumar Taiwan da ta hanzarta aikin musanyar amfanin gona a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan

cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na Taiwan suka bayar, an ce, a ran 19 ga wata, wasu 'yan jam'iyyar the People First Party ta Taiwan (PFP) sun shirya taron manema labaru, inda suka amince da matakan da hukumar kwastam ta babban yankin kasar Sin ta dauka kan yadda za a iya shigar da amfanin gona daga yankin Taiwan cikin sauri kuma cikin sauki. Wadannan 'yan PFP sun kuma yi kira ga hukumar Taiwan da kada ta karya wannan dama mai kyau, ya kamata ta hanzarta aikin musanyar amfanin gona a tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan domin zamantakewar manoman Taiwan.

Bugu da kari kuma, wadannan 'yan PFP sun nuna cewa, babban yankin kasar Sin wata muhimmiyar kasuwa ce ga manoman Taiwan. Ya kamata hukumar Taiwan ta kara yin aikin samar wa manoma taimako yadda za su samu labaru cikin daidai lokaci, bai kamata ta ki dukkan manufofin da babban yankin kasar Sin ya gabatar yadda ta saba ba. (Sanusi Chen)