A ran 18 ga wata a birnin Shanghai, Zheng Lizhong, mataimakin direktan ofishin harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya kamata sassan noma na gabobin 2 sun yada matsayin rinjaye na kansu, su yi mu'amala a tsakaninsu, da kara hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare.
A gun wanin taron manema labarum da aka yi a wannan rana, Mr. Zheng ya ce, gabobin 2 suna kusa da juna, hanyoyin da ake bi wajen sha'anin noma kamar iri daya ne.
Ya bayyana cewa, babban yankin kasar Sin yana son yin kokarin ciyar da mu'amala da hadin gwiwar da ake yi tsakanin gabobin 2 wajen sha'anin noma gaba, sa'an nan kuma yana maraba da mutanen sassan sha'anin noma na Taiwan da su zo babban yankin kasar Sin don bunkasa sha'aninsu, kuma za a kiyaye halallen ikonsu bisa shari'a, da samar musu da muhalli mai kyau don bunkasa sha'aninsu. (Umaru)
|