A ran 17 ga watan Yuli, Ma Yingjiu wanda ya ci zaben shugaban jam'iyyar KMT ya buga waya ga shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao, inda ya gode wa Hu Jintao sabo da taya murna da ya yi masa bayan da ya ci zaben.
A cikin wayar, Ma Yingjiu ya bayyana cewa, bayan da ya hau kan kujerar shugaban jam'iyyar KMT, jam'iyyun nan biyu za su ci gaba da bin makasudai biyar da aka kulla tsakanin shugaban jam'iyyar KMT Lien Chan da shugaba Hu Jintao a yayin da suke shawarwari a ran 29 ga watan Afrilu da ya gabata, don karfafa mu'amala tsakanin jam'iyyun biyu da kuma inganta zaman lafiya da albarka da bunkasuwa a gabobi biyu na zirin Taiwan, ta yadda za a samar wa 'yan uwa na gabobin biyu alheri.(Lubabatu Lei)
|