
A yau ran 13 ga wata da yamma, tawagar wakilan jam'iyyar New Party da ta kawo ziyara a babban yankin kasar Sin a karkashin jagorancin shugaba Yu Muming don tunawa da cikon shekaru 60 da aka cimma nasarar yakin kin harin Japan, ta kammala ziyara a babban yankin kasar Sin, kuma ta dawo Taiwan daga nan Beijing.
Kafin ya tashi, Mr.Yu ya bayar da wani gajeren jawabi cewa, an sami nasarori da dama a wannan ziyara. Ya kuma yi fatan ziyarar za ta ba da taimako wajen karfafa ra'ayin jama'ar gabobin biyu na zirin Taiwan dangane da al'ummar kasar Sin, ta yadda za a samu kyakkyawar makomar al'ummar.(Lubabatu Lei)
|