
A ran 11 ga wata da safe, Mr. Yok Mu-ming, shugaban Sabuwar Jam'iyya na Taiwan da kungiyarsa ta kawo wa babban yankin ziyara domin tunawa da ranar cikon shekaru 60 da cin nasarar yakin kin harin Japan ta jam'iyyar sun ziyarci gadar Lu Gouqiao da dakin tunawa da yakin kin harin Japan da ke kudu maso yammacin birnin Beijing.
A ran 7 ga watan Yuli na shekarar 1937, ba zato ba tsammani ne sojojin kasar Japan suka kai hari kan gadar Lu Gouqiao dake kudu maso yammacin birnin Beijing. Ba tare da kasala ba sai jama'a da sojojin kasar Sin suka yi kukan kura domin yaki da sojojin kasar Japan. Wannan ya alamantar da cewa yakin dagiya na jama'ar kasar Sin kan harin Japan da ya shafe shekaru 8 ana yinsa ya fara.
A shekarar 1993 ce, aka kafa Sabuwar Jam'iyya a Taiwan. Wannan jam'iyya tana bin manufar Sin daya tak, kuma tana yin fama da yunkurin neman 'yancin kan Taiwan. Tana fatan za a ciyar da dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan gaba. (Sanusi Chen)
|