
A ran 6 ga wata da yamma a birnin Guangzhou, sakataren kwamitin Jam'iyyar kwaminis ta Sin ta lardin Guangdong wato Zhang Dejiang ya gana da kungiyar wakilan Jam'iyyar New Party da shugaban jam'iyyar wato Yu Muming ke shugabanta don tuna da ranar cikon shekaru 60 na samun nasarar yakin harin Japan.
Zhang Dejiang ya yi maraba ga kungiyar inda ya ce, wannan ziyarar da kungiyar ta yi ta bayyana ra'ayin 'yan uwanmu na Taiwan sosai wajen kiyaye mulkin kai da cikakken yankin kasar Sin, da kuma burin 'yan uwanmu na Taiwan wajen farfado da kasar Sin. Mr Zhang ya ci gaba da cewa, lardin Guangdong zai ci gaba da yin kokarinsa wajen sa kaimi ga yin mu'amala da hadin kai a tsakaninsa da Taiwan.(Danladi)
|