
Kwamitin zabe na kasar Guinea Bissau ya bayar da sanarwa a ran 29 ga watan nan, cewa za a fara jefa kuri'a a zagaye na biyu na babban zaben shugaban kasar a ran 24 ga watan Yuli.
'yan takara biyu da suka shiga babban zaben shugaban kasar na zagaye na biyu su ne Mr. Sanha, dan takara na jam'iyyar the African Party for the Independence of Guinea-Bissau and Cape Verde wadda ke kan karagar mulki ta kasar da kuma Mr. Vieira, tsohon shugaban kasar. Wani jami'in kwamitin zabe na kasar ya bayyana cewa, kasashen duniya sun riga sun samar da isassun kudade ga babban zaben shugaban kasar a zagaye na biyu domin tabbatar da cimma narasa a cikin zaben nan.(Kande Gao)
|