
Mun sami labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ran 27 ga wata a birnin Wuhan na jihar Hubei, an bude taron makon Taiwan na birnin Wuhan da ke lardin Hubei na karo na 2. A wannan rana, yawan abubuwan da Wuhan da Taiwan suka sa hannua kai ya kai guda 11, jimlar kudin da aka zuba jari ya kai misalin yuan biliyan 0.26, inda suka shafi fanin kayayyakin gine-gine, da abinci, da sadarwa ta hanyar komfuta, da sarrafe sarrafe da kuma aikin noma, da dai sauransu.
Bisa labarin da muka samu an ce, za a kammala wannan taro a ran 2 ga wata mai zuwa. 'Yan kasuwa sama da 150 wadanda su ka fito daga tsibirin Taiwan da shiyyoyin Turai da na Amurka sun halarci taron. (Bilkisu)
|