|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-06-24 17:30:33
|
 |
Jam'iyyar PRS ta kasar Guinea-Bissau ta ki amincewa da sakamakon babban zabe na zagaye na farko
cri
Mun sami labari daga kamfanin dilancin labaru na Xinhua cewa, ran 23 ga wata, jam'iyyar PRS ta kasar Guinea-Bissau, wadda ke karkashin shugabancin Kumba Yalla, wato tsohon shugaban kasar kuma 'dan takarar neman shugaban kasar na yanzu, ta sanar da cewa ba za ta amince da sakamakon babban zabe na zagaye na farko na kasar Guinea-Bissau ba, kuma ta bayyana cewa, za ta bukaci canja sakamakon zaben.
Jam'iyyar PRS tana ganin cewa, sakamakon zaben shugaban kasa na zagaye na farko da kwamitin zabe na dukan kasar yabayar ba daidai ba ne, an yi magudi a lokacin da aka jefa kuria,don haka za ta daukaka kara.
Bisa sakamakon babban zabe na zagaye na farko da kwamitin zaben duka kasar Guiea-Bissau ya bayar an ce, yawan kuri'un da Malam Bacai Sanha, wato 'dan takarar kungiyar PAIGC ya samu ya fi na sauran 'yan takara, Kumba Yalla ya kai matsayi na 3. Sabo da babu 'dan takarar da ya iya samun kuri'u sama da rabi, bisa dokar zabe, 'yan taka biyu da yawan kuri'un da suka samu ya fi yawa za su ci gaba da takara zaben shugaba bayan kwanaki 21 da suka wuce, wato bayan bayar da sakamakon zabe na zagaye na farko. (Bilkisu)
|
|
|