A ran 23 ga wata, 'yan majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu 5 wadanda ake zarginsu da hannu a cikin wata matsalar rashawa sun yi murabus daga mukamansu. Sabo da haka, sun zama sauran manyan 'yan siyasa bayan tsohon shugaba Jacob Zuma na kasar wadanda kura ta rutsa da su a cikin aikin kawar da rashawa da al'amubazzaranci.
Wadannan 'yan majalisar dukkansu membobin jam'iyyar babban taro na jama'ar Afirka na Afirka ta Kudu. Kakakin jam'iyyar ya ce, yanzu wadannan 'yan majalisar suna jin kunya domin abubuwan da suka yi sun yi mummunar tasiri ga majalisar dokokin kasar da jam'iyyar da suke ciki. Ko da yake sun yi murabus daga mukaminsu, amma, dole ne za a yanke musu hukunci bisa dokoki. (Sanusi Chen)
|