A ran 23 ga wata a birnin Algeirs, babban birnin kasar Aljeriya, ministan gudanarwa kuma ministan harkokin waje na kasar Muhammad Bedjaoui ya bayyana cewa, kasar Aljeriya tana son kwantar da kura a tsakaninta da Morocco, kuma tana son maido da dangantakar abuta da ke tsakaninta da kasar Morocco.
A gun taron manema labaru da aka shirya a ran nan, Mr Bedjaoui ya ce, kasar Aljeriya tana son bunkasa dangantakar da ke tsakaninta da kasar Morocco, bai kamata a yi la'akari da tasirin da kungiyar kawancen jama'ar yammacin Sahara ta yi musu ba. Haka kuma ya yi kira ga kasashen biyu da su kawar da bambancin ra'ayoyinsu domin kago sharadi ga ganawar da shugabannin kasashen suka yi wa juna.(Danladi)
|