Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-06-23 17:26:59    
Kasar Guinea-Bissau ta gamu da barkewar kwalara inda ya sa mutane 6 suka rasa rayukansu

cri
Mun sami labari daga kamfanin dilancin labaru na Xinhua cewa, 'yan kwanakin da suka wuce, a kasar Guinea-Bissau an sami barkewar kwalara, tun daga ran 11 ga watan Yuni har zuwa yanzu, akwai mutane 194 da suka kamu da ciwon nan, inda mutane 6 sun mutu.

Kungiyar aikin likita ta kasar Sin da ke kasar Guinea-Bissau ta tabbatar da wannan labari, kuma ta nuna cewa, yanzu tana yin kokarin ba da taimako ga kasar don shawo kan kwalara.

Bisa labari daban da kafofin labaru na kasar Guinea-Bissau ya bayar an ce, asibitin Bissau da ke babban birnin kasar yana ceton masu ciwon kwalara, an kimanta cewa, a kwanaki masu zuwa nan gaba, watakila yawan masu ciwon nan zai karu.

Hukumomin kiwon lafiya na kasar Guinea-Bissau suna ganin cewa, watakila ciwon kwalara yana yaduwa ne daga kasar Senegal, wato kasar da ke makwabtaka da ita.. (Bilkisu)