Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-06-21 17:13:51    
An kafa sabuwar gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya

cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka bayar, an ce, a ran 19 ga wata an riga an kafa sabuwar gwamnatin kasar wadda ke karkashin jagorancin sabon firayin minista Elie Dote.

An kafa wannan sabuwar gwamnati ne bayan da Francois Bozize ya ci zaben shugaban kasar a ran 8 ga watan Mayu. Wannan sabuwar gwamnati tana kunshe da firayin minista da kananan ministoci 3 da ministoci 18 da wakilai 5 wadanda suke matsayin ministan gwamnati. Shugaba Francois Bozize ya ci gaba da zama a kan mukamin ministan tsaron kasar kamar yadda ya saba.

Kaddamar da sabuwar gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta almantar da cewa, an kawo karshen gwamnatin wucin gadi da aka kafa bayan da janar Bozize ya yi juyin juya hali a watan Maris na shekarar 2003. (Sanusi Chen)