Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-06-21 09:21:51    
'Yan kallo na duniya sun amince da ayyukan kada kuri'a da aka yi cikin zaben shugaban kasa na Guinea Bissau

cri

A ran 20 ga wata a birnin Bissau,babban birnin kasar Guinea Bissau,'yan kallo na duniya wadanda suka dauki nauyin sa ido kan zaben shugaban kasar Guinea Bissau sun nuna amincewarsu ga aikin kada kuri'a da aka yi cikin zaben shugaban kasa.

'Yan kallo sama da meta na duniya da suka zo daga kungiyar tarayyar kasashen Turai da kungiyar tarayyar Afrika da sauran kungiyoyin duniya da kasashe sun sa ido kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa na Guinea Bissau.Sun bayyana cewa hanyar da aka bi wajen kada kuri'a a ran 19 ga wata ta fito fili,kuma ta dace da ma'aunin duniya da lamarin ya shafa.'Yan kallo na duniya sun kuma yaba wa rundunar sojan Guinea Bissau kan matsayin 'yan ba ruwanmu da ta dauka cikin zaben shugaban kasa.(Ali)