
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , A ran 15 ga wata a nan birnin Beijing , Li Weiyi , kakakin Ofishin harkokin Taiwan na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa , Babban yankin kasar Sin ba zai sauya ra'ayinsa sa kaimi kan aikin shatan jiragen sama a tsakanin gabobi biyu na Tekun Taiwan . Muddin aikin yana da amfani ga 'yan uwa na Taiwan , kuma yana da amfani ga yin musanyar tsakanin bangarorin biyu , to , bangaren babban yanki zai yi kokarin yinsa .
Mr. Li ya bayyana cewa , ya yi fatan hukumomin kula da wannan aiki na Taiwan su kasa yin haka da kowane dalili . Sa'an nan kuma bangaren babban yanki yana son musanya ra'ayoyi da bangaren Taiwan kan batun shatan jiragen sama . ( Ado)
|