Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-06-14 21:02:43    
Yan asalin Taiwan na Sin sun gamu da wahala wajen neman komar da allunan sunayen kakanninsu gida daga haikalin Yusukuni

cri
Ran 14 ga wata da safe, kungiyar wakilan 'yan asalin Taiwan na kasar Sin sun je haikalin Yusukuni na Japan don neman komar da allunan sunayen kakaninsu gida daga wannan haikalin. Amma wannan kungiyar wakilai ba ta sami damar shiga cikin haikalin nan ba sabo da hani da 'yan tsageru da 'yan sanda na kasar Japan suka yi.

Kungiyar wakilan nan da ke kunshe da mutane 60 ta sauka birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan a ran 13 ga wata. A lokacin ziyarar mako daya, kungiyar wakilan za ta nemi haikalin Yusukuni da ya kawar da allunan sunayen kakannin 'yan asalin Taiwan na Sin daga haikalin nan da sauransu. A haikalin nan an ajiye allunan sunayen manyan masu laifuffukan yaki. (Halilu)