Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-06-02 09:47:54    
Kenya ta yi bikin murnar ranar samun ikon tafiyar da harkokinta da kanta

cri

Gwamnatin kasar Kenya ta yi bikin murna a birnin Nairobi, hedkwatar kasar a ran 1 ga watan Yuni, don murnar zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar.

An yi bikin murna ne a filin wasa na duniya da ke birnin Nairobi. Shugaban kasar Mwai Kibaki da manyan jami'an gwamnatin kasar da na soja da mutane dubai daga wurare daban daban na kasar ne sun taya murna tare.

A cikin jawabin da ya bayar, shugaba Kibaki ya bayyana cewa, tun ran 1 ga watan Yuni na shekarar 1963 har zuwa yanzu, ba a iya hana kasar Kenya ta nemi samun cikakken 'yancin kai ba. Ya kuma yi kira ga al'ummar kasarsa da su ci gaba da daukan nauyin gina kasarsu, a karkashin ra'ayin 'ranar samun ikon tafiyar da harkokinta da kanta'.(Tasallah)