
Wakiliyar Rediyon kasar Sin ta ruwaito mana labari cewa , a ran 1 ga watan nan a nan birnin Beijing , Tang Yi , mataimakin shugaban Hukumar tattalin arziki ta Ofishin harkokin Taiwan na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa , a cikin wani lokacin da ya wuce , hukumomin da abin ya shafa na babban yankin Kasar Sin sun tattauna kuma sun yi nazarin manufofi da matsalar fasahohin sayar da kayayyakin noma na Taiwan a babban yankin , wato sun yi ayyukan share fage masu yawa don sa kaimi kan sayar da kayayyakin noman .
A gun taron watsa labarun da aka shirya a wannan rana , Mr. Tang ya bayyana cewa , a farkon watan jiya babban yamkin ya sanar da cewa , yawan 'ya'yan itatuwan Taiwan da aka ba su izinin shigo ya karu daga ire-ire 12 zuwa 18 , kuma an soke kudin haraji ga 'ya'yan itatuwa 10 dake cikinsu . (Ado )
|