
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Congo(Kinshasa) ya bayar a ran 31 ga watan Mayu, an ce, jam'iyyar da shugaban kasar Congo(Kinshasa) Joseph Kabila ke jagoranci ta gabatar da shi da ya zama dan takarar neman zaman shugaban kasar a kwanan baya, wanda shekarunsa 33 da haihuwa.
Kakakin Mr. Kabila ya bayyana cewa, shugaba Kabila bai bayyana ra'ayinsa kan wannan ba tukuna, idan lokaci ya yi, to, Mr. Kabila zai sanar da ko zai shiga babban zaben shugaban kasar ko a'a. (Tasallah)
|