A ran 31 ga watan nan ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta yanke hukunci cewa, kwalin da kasar Amurka da Thailand da Korea ta kudu da Taiwan ke sayar wa kasar Sin sun cika yawa, kuma ta tsai da kudurin kuntata yawan kwalin da za a shigo da su daga wadannan wurare.
Ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta bayar da sanarwa a ran nan cewa, bisa binciken da aka yi an ce, yawan kwalin da aka saya daga wadannan wurare ya cika yawa, kuma ya tauye moriyar masana'antar yin kwali na kasar Sin, sabo da haka kasar Sin ta tsai da kudurin kuntata yawan kwalin da za a shigo da su daga wadannan wurare. (Dogonyaro)
|