|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-05-27 17:50:38
|
 |
Kenya ta yi fatan kafofin watsa labaru na kasar Sin za su ba da babban taimako a wajen watsa labarun Afrika
cri
 Wakilin Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ruwaito mana labari cewa , a ran 26 ga watan nan Jorge Opio , shugaban Hukumar watsa labaru ta kasar Kenya kuma shugaban Kamfanin dillancin labaru na kasar ya ce , lokacin da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke watsa labarun Afrika , su kan lura da abubuwa marasa kyau kuma su kan habaka girman tasirinsu . Ya yi fatan kafofin watsa labaru na kasar Sin za su ba da babban taimako a wajen watsa labarun Afrika , ta yadda za a sa kasashen duniya su gane yalwatuwa da ci gaban kasashen Afrika kuma su ba da taimako ga kasashen Afrika a wajen fid da kai daga tasiri maras kyau wanda labarun da kasashen Yamma suka watsa bisa rashin adalci suka kawo .
A wannan rana Mu'atu , kakakin gwamnatin kasar Kenya ya ce , kafofin watsa labaru ba kawai suna watsa labarun Afrika cikin rashin adalci ba , har ma suna yin haka kan kasashe matasa masu yawa . (Ado)

|
|
|