Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar, an ce, a ran 26 ga wata a birnin Bamako, an rufe taron tattaunawa kan yadda za a yi fama da taskun da ake nuna a cikin iyalai a yankunan yammacin Afirka, inda aka nemi kasashen Afirka da su bi dokokin hana yin manyan hukunce-hukunce kan yara da yin fama da nuna tasku a cikin iyalai kuma da su girmama iko iri iri na yara.
Asusun yara na M.D.D da gwamnatin kasar Mali ne suka shirya wannan taron da aka shafe kwanaki 3 ana yinsa a Bamako, babban birnin kasar Mali.
A gun taron, wakilai sun ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatocin kasashen Afirka su kara ware kasafin kudi domin kawar da yara daga taskun da ake nuna musu.
A gun bikin rufe taron, minista mai kula da mata da yara da iyalai ta kasar Mali malama Berthe Aissata Bengaly ta ce, a gun wannan taron tattaunawa, wakilai sun fahimci matsalar nuna tasku kan yara sosai da take kasancewa a yankin yammacin Afirka, kuma sun amince da hanyoyi da matakan warwarewar wadannan matsaloli.
Wakilai fiye da dari 2 na gwamnatocin kasashe 24 da na kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun halarci taron. (Sanusi Chen)

|