Ran 25 ga wata, kwamitin kungiyar EU ya bayar da sanarwa cewa, jami'a mai kula da huldar waje da manufofin makwabcinta Madam Waldner ta kai ziyara a Libya a ran 24 da ran 25.
Sanarwar ta ce, Madam Waldner ta yi tattaunawa tare da shugaban kasar Libya Khadafi da firayin ministan kasar Chanem, bangarorin biyu sun yi tattaunawa kan kara bunkasa huldar da ke tsakaninsu. Ban da haka kuma Waldner ta yi tattaunawa tare da shugabannin kasar kan maganar Libya ta yi hukuncin kisa ga masu ba da agaji na Romania da na Palesdinu. [Musa]

|