Shugaban kasar Uganda Yoweiri Kaguta Museveni ya yi wa kasashen yamma zargin yunkurin sa hannu cikin harkokin gida na kasarsa ta hanyar ba da taimakon bunkasuwa.
Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Uganda suka bayar, an ce, Mr. Museveni ya yi wa wasu kasashen yamma masu ba da taimako sukan matsa wa kasarsa lamba, ta hanyar barazanar rage taimakon bunkasuwa da suka bayar. Ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa za ta yi tattaunawa da wadannan kasashen yamma kan batun dimokuradiyya, amma ba za ta mayar da batutuwan siyasa da tattalin arziki da al'adu nata kamar sharuddan da ta bayar don samun bunkasuwa.(Tasallah)

|