
Daga ran 25 ga watan nan a kasar Masar an fara jefa kuri'ar raba gardama kan shirin gyara babi na 76 na tsarin mulki na zaben shugaban kasa.
Bisa labarin da aka samu an ce, yawan halallun masu zaben da suka yi rajasta a Masar ya kai miliyan 32. ma'aikatar harkokin gida ta Masar ta shirya wurare fiye da dubu 50 na jefa kuri'a a duk kasa, za a jefa kuri'a daga karfe 8 da safe zuwa karfe 7 da yamma. Za a bayar da sakamako a daren ran nan, kuma za a bayar da sakamako a hukunce a ran 26 ga watan nan. (Dogonyaro)

|