
A ran 20 ga wata a nan birnin Beijing,mataimakin darektan ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mista Wang Zaixi ya bayyana cewa kamata ya yi a tabbatar da ra'ayoyin bai daya da sakatare-janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Hu Jintao da shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin Lien Chan da shugaban jam'iyyar people first party James Soong suka samu,a yi kokarin ciyar da dangantaka dake tsakanin bangarorin biyu dab da zirin teku na Taiwan ta dosa wa gaba a kan hanyar sassauci.
A gun taron duniya na uku na sada zumunci tsakanin kungiyoyin sinnawa masu zama a kasashen ketare da aka yi,Mista Wang Zaixi ya ce gwamnatin kasar Sin za ta cigaba da bin muhimmiyar manufar "dinke mahaifa cikin lumana da kasa daya da tsarin mulki biyu",ta cigaba da bin ka'idar Sin daya,ta yi adawa da dukkan ayyukan neman balle Taiwan daga kasar Sin,ta cigaba da fadada mu'amala tsakanin jama'a na bangarorin biyu wadda habaka mu'amala wajen tattalin arziki da ciniki ke cibiyarta,ta cigaba da bin ka'idar sa fata ga mutanen Taiwan.(Ali)
|