
A ran 15 ga watan nan jiragen ruwan daukar kaya na Taiwan da Hong Kong sun yi sufurin 'ya'yan itatuwa da amfanin gona kusan Ton 50 na kudancin Taiwan zuwa Fuzhou, hedkwatar lardin Fujian a kudu maso gabashin babban yankin kasar Sin. Wanann shi ne karo na farko da aka yin sufurin amfanin gona daga kudancin Taiwan zuwa babban yankin kasar Sin.
An bayyana cewa, an yi sufurin wannan tarin amfanin gona daga kudancin Taiwan ne bisa yarjejeniyar da wani kamfanin babban yaki da wani kamfani na Taiwan suka kulla, kuma za su ci gaba da sa kaimi ga sufurin amfanin gona daga Taiwan zuwa lardin Fujian. (Dogonyaro)
|