
A ran 12 ga wannan wata a nan birnin Beijing, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban jam'iyyar da ake kira '"The People First Party" James Soong da kungiyar wakilan jam'iyyar da ke yin ziyara a babban yankin kasar Sin a karkashin jagorancinsa.
Mr Hu jintao ya bayyana cewa, neman zaman lafiya da neman zaman karko da kuma neman raya kasa, fata iri daya ne da 'yanuwan bangarorin biyu da ke Zirin Taiwan suka yi, bisa matsayin shugabannin jam'iyyun da ke bangarorin biyu , ya kamata su bi sawun zamanin yau da kuma amince da niyyar jama'a har da yin aiki wurjanjan don yin kokarin cim ma buri na sake farfado da al'ummar kasar Sin. Ya ce, yanzu, huldar da ke tsakanin bangarorin biyu ta sami bunkasuwa zuwa wani sabon lokaci mai muhimmanci, ya kamata jam'iyyun biyu su yi aiki mai yakini don bayyana wa 'yanuwan bangarorin biyu makoma mai kyau wajen raya huldar da ke tsakanin bangarorin biyu cikin zaman lafiya da zaman karko da kuma bayyana wa duniya cewa, Sinawa suna da karfi da hazikanci wajen daidaita sabani da bambanci da ke kasancewa a tsakanin bangarorin biyu na Zirin Taiwan.
Hu Jintao ya sake jaddada cewa, muddin a amince da ka'idar Sin daya tak a duniya, da kuma amince da ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992, to, kome mutumi, kome jam'iyya , kome magana da ya bayyana da kuma kome aiki da ya taba yi , mu ma muna son yin shawarwari da su a kan batun raya huldar da ke tsakanin bangarorin biyu da na sa kaimi ga dinkuwar kasa gu daya.
Mr James Soong ya bayyana cewa, sauye-sauye da ci gaba da babban yankin kasar Sin ya samu tun daga ranar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa ya sa mutane sun faranta rai sosai. Ya bayyana cewa, jam'iyyarsa ta nace ga tsayawa kan matsayi mai ka'idoji uku wato nuna goyon baya ga ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992, da yin adawa da neman 'yancin Taiwan da kishin zaman lafiya ba tare da kasala ba.Yana ganin cewa, bangarorin biyu za su iya samun sakamako mafi kyau a cikin muhallin zaman lafiya.(Halima)
|