Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-11 15:38:19    
An gamu da matsaloli wajen sake gina tsarin siyasa a kasar Iraq

cri
Bayan da majalisar dokokin kasar Iraq ta amince da sababbin 'yan majalisar ministoci 6, gwamnatin rikon kwarya ta kasar Iraq ta sake kira bikin yin rantsuwar kama aiki a ran 9 ga watan nan a karo na 2, haka kuma sabuwar majalisar ministoci ta shirya taro na farko na ayyuka. Haka yanzu ba a tabbatar da ministan kula da harkokin hakkin dan Adam da kuma wani mataimakin firayin ministan kasar ba kawai. Bayan watanni misalin 3 da aka yi babban zaben shugaban kasar, yanzu a karshe dai kasar Iraq ta kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya, wannan muhimmin mataki ne da kasar Iraq ta dauka wajen sake gina tsarin siyasa.

Game da dalilin da ya sa gwamnatin wucin gadi ta kasar ta sake kira bikin yin rantsuwar kama aiki, wani jami'in kasar Iraq ya yi bayani cewa, akwai dalilai guda 2, na farko shi ne lokacin da sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta kasar ta yi bikin yin rantsuwar kama aiki a karo na farko a ran 3 ga watan nan, saboda mutane masu darikar shi'ite da Kurdawa sun ki amincewa da 'yan majalisar ministoci masu darikar sunni, ta haka Mr. Ibrahim al-Jaafari bai tabbatar da 'yan majalisar ministoci 7 da ke cikin dukan 'yan majalisar 37 ba. Na biyu kuma shi ne Kurdawa sun nuna rashin jin dadinsu saboda ba a tanada 'kasar Iraq tarayyar kasa ce ta dimokuradiyya' a cikin jawabin yin rantsuwar kama aiki na farko. Amma an yi watanni fiye da 3 ana kammala babban zaben shugaban kasar da kuma kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar a hukunce, wannan ya shaida cewa, ana gamu da matsaloli da yawa wajen sake gina tsarin siyasa a kasar Iraq a bayyane.

Da farko, muhimmin dalilin da ya sa aka fama da matsala wajen sake gina tsarin siyasa a kasar Iraq shi ne saboda rikicin da ke tsakanin mutanen kasar a fannonin al'umma da addinai. Babban zaben shugaban kasar da aka yi ya canja daidaiton karfin siyasa na kasar. Bayan da aka kammala babban zaben, manyan rukunnoni na masu darikar shi'ite da Kurdawa da kuma masu darikar sunni sun yi ta gardama kan manyan ministocin kasar da kuma yadda za a raba iko a nan gaba, wannann ya haddasa gwamnatin wucin gadi ta kasar ta dade ba ta kafa majalisar ministocinta ba.

Wani dalili daban shi ne saboda an rasa isasshen tushe a cikin kasar Iraq a fannin siyasa ta dimokuradiyya. Jama'ar kasar Iraq suna neman shimfida dimokuradiyya a kasarsu. Duk da haka, tilas ne jama'ar kasa suna so a shimfida dimokuradiyya a kasarsu, a sa'i daya kuma, tilas ne a yi la'akari da halin musamman na ko wace kasa da kuma halin da suke ciki. Kasar Iraq ta yi shekaru goma gomai tana karkashin mulkin kama karya na Sadam, ko kusa wani yaki ya tilasta mata a kan hanyar dimokuradiyya a cikin dare guda. Ma iya cewa, an rasa isassun hali da kuma tushe wajen shimfida dimokuradiyya a kasar Iraq. A cikin wannan hali ne, mun fahimci cewa, ana shimfida dimokuradiyya a kasar a hankali a hankali, har ma ana gamu da matsaloli da yawa.

Ko da yake haka ne, amma a karshe dai an kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a kasar Iraq, wannan ya bayyana cewa, rukunnonin siyasa daban daban na kasar sun iya dora muhimmanci kan moriyar kasarsu, sun yi rangwame, sun sami ra'ayi daya. Kafuwar sabuwar gwamnatin kasar yana da muhimmanci sosai a fannonin shimfida kwanciyar hankali da kuma samun cikakken zaman kan kasar, yawancin kasashen duniya suna jin dadi kan wannan. Yau bayan da shekaru 2 da aka sa aya ga yakin Iraq, mutane suna fatan sabuwar gwamnatin kasar Iraq za ta iya dauki babban nauyi kan wuyanta, za ta kuma shugabanci kasar da ta fita daga mawuyancin hali, za ta shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Tasallah)