
A ran 9 ga watan Mayu,shugaban jam'iyyar people first party wanda ke ja ragamar ziyarar babban yankin kasa tare da iyalinsa ya kai ziyarar ban girma a gaban kabaran kakanin-kakaninsa.Wannan karo ne na farko da iyalin James Song ya kai ziyarar ban girma ga kakanin-kakaninsu tun bayan shekara ta 1949.
Bayan nuna girmamawa,James Song ya yi takaitaccen jawabi inda ya nuna godiyarsa kan shirye shiryen da mutanen wurin suka yi dominsa,kuma ya yi farin ciki da ganin manyan sauye sauyen da aka samu cikin shekaru sama da hamsin da suka gabata.(Ali)
|