Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-09 08:36:58    
Mr.Yang Zhengwu ya gana da Mr.James Soong

cri

A ran 8 ga wata da dare,a birnin Changsha,sakataren kwamitin lardin Hunan na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin Yang Zhengwu ya gana da `yan kungiyar yin ziyara a babban yankin kasar Sin ta jam`iyyar PFP wadda ke karkashin shugabancin shugaban jam`iyyar James Soong kuma ya shirya walima dominsu.

Mr.Yang Zhengwu ya ce,shugaba James Soong na jam`iyyar PFP ya kai ziyara a babban yankin kasar Sin tare da `yan kungiyarsa,wannan ne babban al`amari na `yan uwa na al`ummar kasar Sin,jama`ar lardin Hunan sun fi mai da hankali kan wannan saboda garin shugaba James Soong a lardin Hunan yake.Shugaba Soong ya nace ga ka`idar kasar Sin daya tak a duniya,kuma ya nuna kiyayya ga `yancin kan Taiwan,jama`ar garinsa suna jin farin ciki.

Mr.James Soong ya ce,yana kishin Taiwan,kuma yana kishin kasar Sin saboda shi ne `dan kasar Sin.Kamata ya yi jama`ar gabobi biyu na zirin Taiwan su gama kansu kuma su yi kokari tare don kago makoma mai haske ta jama`ar kasar Sin a karni na 21.(Jamila Zhou)