Ran 8 ga wata da maraice, kungiyar ziyara ta Jam'iyyar The People First Party wadda ke karkashin jagorancin Mista James Soong, shugaban jam'iyyar ta isa lardin Hunan don ci gaba da yin ziyara a babban yankin kasar Sin.
Kungiyar Soong tana yin ziyara a babban yankin kasar Sin ne bisa gayyatar da kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Mista Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar suka yi musu. Lardin Hunan tsohon wuri na kaka-kakanin Mista Soony ne. An labarta cewa, a lokacin da yake a lardin nan, Mista Soony zai gana da jami'an kwamitin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a lardin Hunan, kuma zai je birnin Xiang Tan don yin ta'aziyya ga kaka-kakkaninsa a ran 9 ga wata, kuma zai ziyarci makarantar firamare inda ya taba yin karatunsa.
Kafin saukarta a lardin Hunan, kungiyar ziyarar ta kai ziyarar ban girma ga Wang Daohan, shugban kungiyar kula da hulda tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan a birnin Shanghai a safiyar wannan rana. A lokacin da yake zantawa da wakilan 'yan kasuwa na Taiwan na wurare daban daban a birnin Shanghai a tsakar wannan rana, Mista Soony ya bayyana cewa, jam'iyyarsa tana tsayawa tsayin daka wajen yin adawa da abu na wai 'yancin kan Taiwan. (Halilu)
|